Hanyar Kano

Hanyar Kano Domin sanin halin da hanyoyin Kano ke ciki, don kaucewa cunkoso, samun bayanai kan yanayin tsaro…

Kun tuna da wannan sha-tale-talen da ake ginawa a bakin gadar Kofar Nasarawa, maimakon wanda aka rushe na kofar gidan gw...
17/05/2026

Kun tuna da wannan sha-tale-talen da ake ginawa a bakin gadar Kofar Nasarawa, maimakon wanda aka rushe na kofar gidan gwamnatin Kano?

Me ya sa aikin ke tafiyar hawainiya?

Titin Dakata Kwanar Kotu na bukatar dauki, sakamakon tsawon lokacin da ya shafe a lalace. Ma’abota bin hanyar na fargaba...
17/05/2026

Titin Dakata Kwanar Kotu na bukatar dauki, sakamakon tsawon lokacin da ya shafe a lalace.

Ma’abota bin hanyar na fargabar yadda zuwan Damuna zai sanyasu cikin hadari, saboda rashin magudanan ruwa da kuma yadda hanyar ke jagulewa.

Lokacin Daukar Hoto: Asabar 16/05/2026, 10:20am

17/05/2026

Titin Hadejia Road zuwa Sha-tale-talen Kano Club da yammacin ranar Asabar, 16-05-2026.

Cikin Hotuna: Yadda aikin titin Chalawa, Gundumi,Kwanar Zaura, Rafin Damo, Kadiyawa, Gandu, Adaraye da Zaura Fulani, Yad...
16/05/2026

Cikin Hotuna: Yadda aikin titin Chalawa, Gundumi,Kwanar Zaura, Rafin Damo, Kadiyawa, Gandu, Adaraye da Zaura Fulani, Yada kunya da kuma Bele ke gudana.

Duk wadannan yankuna na karkashin Karamar Hukumar Ungogo.

Lokacin Daukar Hoto: Juma’a, 15-05-2026

07/05/2026

Me wannan titin na Zoo Road ke tuna muku a duk lokacin da kuka ketara ta hanyar?

Cikin Hotuna: Yadda aka ‘kawata sha-tale-talen gidan Baban Gwari da ke birnin Kano.
07/05/2026

Cikin Hotuna: Yadda aka ‘kawata sha-tale-talen gidan Baban Gwari da ke birnin Kano.

04/05/2026

Yadda titin State Road ya kasance a Litinin dinnan, 04-05-2026.

@12:30pm

‎Al'ummar kananan hukumomin Sumaila da Takai na ci gaba da kokawa kan lalacewar hanyar Magami zuwa Tukuda da kuma  babba...
04/05/2026

‎Al'ummar kananan hukumomin Sumaila da Takai na ci gaba da kokawa kan lalacewar hanyar Magami zuwa Tukuda da kuma babbar hanyar Birnin Bako zuwa Takai.

‎Atiku da Saura na daga cikin mazauna garin ya bayyana mana cewa hanyar Birnin Bako zuwa Takai babbar hanya ce. Ita ce ta haɗa dukkan ƙauyukan Takai da gari. Ita ce cibiyar kasuwanci da lafiyarsu amma hanyar ta zama taron mutuwa a yanzu.

‎Haka kuma sun bayyana cewa sakamakon rashin hanyar suna tafka asara a gonakinsu na amfanin da suke samarwa

‎Mazauna yankin sun roki Gwaman Kano Abba Kabir Yusuf da Sanatan Kano ta kudu Kawo Sumaila da "yan majalisun su na jiha dana tarayya dasu kawo musu dauki, sakamakon karatowar damina

📷 Premier Radio

Ana samun korafi daga ma’abota bin hanyar Iyaka Road da ke bayan Sakatariyar Audu Bako, sabida aikin raba hanyar ba tare...
04/05/2026

Ana samun korafi daga ma’abota bin hanyar Iyaka Road da ke bayan Sakatariyar Audu Bako, sabida aikin raba hanyar ba tare da fadadata ba.

Kamar yadda hotunan s**a nuna, bayan kammala wannan aiki, da yiwuwar hanyar ta rika samun cunkoson ababen hawa, saboda rashin yalwar jerawar akalla motoci 2 a lokaci guda.

Ya kuke gani?

02/05/2026

Da wanne lokaci kuka fi fuskantar cunkoson ababen hawa a wannan hanyar ta Bompai Road?

Me ya sa ake yawan samun aukuwar hadari a gadar Hotoro?Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci gadar, domin gane wa idonsa ha...
01/05/2026

Me ya sa ake yawan samun aukuwar hadari a gadar Hotoro?

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ziyarci gadar, domin gane wa idonsa halin da take ciki, da kuma matakan da za a dauka don shawo kan matsalar.

A ganinku me ke janyo hadari a gadar?

Address

Kano
700001

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hanyar Kano posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share

Category